Tatsuniya: Gizo Da Ƙoki
Story: the spider and his wife
Gizo wants to steal from the garden; Ƙoki wants to ask. A folk tale with the usual closing formula.
Gatanan gatananku
Ta zo mu ji ta.
Wata rana gizo da matarsa ƙoki sun je rafi ɗebo ruwa, sai yunwa ta dame su, suka rasa yadda za su yi. To kusa da rafin akwai lambu, cikin lambun akwai nunannun kayan itatuwa kamar su mangwaro da lemo da ayaba da gwaiba da kuma kankana da dai sauransu, ga su nan ana iya ganinsu daga waje.
Nan da nan sai gizo ya kawo shawara akan su shiga kawai, “su saci na sata su bar na bari”, ai ba mai kallonsu. Ƙoki ta ce a'a gizo, kar mu yi haka, mu je kusa idan mun ga mai gonar mu tambaye shi, idan ya bamu sai mu tsinka, mu mai godiya.
Suna cikin shawara, sai suka ga wata kurciya ta sauko daga saman bishiya, ta fara ba su labarin lambun cewa, a cikin lambun akwai wani dodo, kuma ba ya bari a shiga lambun sai an ba shi man-shanu; sai firr tsuntsuwar ta tashi sama ta wuce.
Gizo da ƙoki suka dubi sama da ƙasa, ba inda za su samu man-shanu, sai gizo ya kawo shawara a kan a nemi man-kaɗe a kaiwa dodo tun da bai san bambancinsu ba. Sai ƙoki ta ce ee a yi hakan, nan da nan sai suka nemi man-kaɗe suka nufi wajen dodon.
Suna shiga, dodo ya ce masu da mai kuka zo min? Sai gizo ya ce mai man-shanu. Gizo ya miƙa masa, yana karɓa ya shinshina sai ya ji warin man-kaɗe. Yana jin haka sai ya ce wa gizo ni za ku yaudara, maza ku fita ku ba ni wuri.
Sai ƙoki ta ce wa gizo su ba shi haƙuri, gizo kuwa bai ƙi shawarar ta ba, suka yi ta ba dodo haƙuri. Can dai sai dodon ya yi haƙuri, ya ce su shiga su ɗebi duk abin da suke so. Nan da nan kuwa suka shiga suka ɗebi na ɗiba har da wanda za su kai gida. Suka fito suna wa dodo godiya.
Ƙarshen tatsuniya
Takurunkus, kan ɓera.
🎯 Aiki-Tambayoyi
- Me sunan tsuntsuwar da ta ba su gizo shawara?
- Wàye ya ke gadin lambun?
- Wasu irin 'ya'yan itatuwa ake samu a lambun?
- Me ake kaiwa dodon?
- Yi bayanin abin da tatsuniyar ke koyarwa a sakin layi biyar.
- Wani suna za ka baiwa tatsuniyar?