Cutar Alaƙaƙai
Corona Virus / COVID-19
Where the virus came from, how it spreads, its signs, and how to guard against it.
Asalin cutar: Cutar ta samo asali ne daga ƙasar China sannan ta yaɗu zuwa sauran ƙasashen duniya ciki har da Nijeriya. An ce a cikin kowane mutum (200) da suka kamu da ita, za ta iya kashe mutum biyu. Wannan shi ya sa ake damuwa a kanta, in ji masana.
Cutar na farawa ne da masassara, sai kuma tari da ke biyo baya, sannan bayan mako ɗaya sai a fara samun wahala wajen shaƙar numfashi. Ta fi mura tsanani domin tana haddasa zazzaɓi mai tsananin gaske kuma tana iya yin kisa. Wannan ya sa gwamnatoci da masana harkar kiwon lafiya tashi haikan domin samo magani da kuma rigakafin cutar.
Yadda cutar ke yaɗuwa: Cuta ce mai saurin yaɗuwa fiye da yadda ake zato, in ji masana. Ana ganin idan mutum ɗaya ya kamu, a cikin yini guda zai iya shafa wa mutum uku zuwa tara. Sannan a cikin kwana shida adadin zai iya ninkawa wajen hawa tara a cikin ƙanƙanin lokaci.
Masanan sun ƙara da cewa, misali idan mutum yana cikin taro, sai ya yi atishawa ko ya yi kaki ya tofar ko kuma ya faɗe majina da hannunsa, to zai iya shasshafa wa mutane ta hannayensu.
Alamomin cutar
Symptoms
- Mura
- Tari
- Ciwon kai
- Tsamin jiki
- Wahala wajen jan numfashi
Matakan kariya daga cutar
Precautions
- A riƙa yawan wanke hannu ko goga man tsaftace hannu (hand sanitizer).
- Waɗanda suke mura su daina shiga cikin taron jama'a ko kuma a ba su hutu har su samu sauƙi.
- A guji yawan taɓa abubuwa a wurare, sannan a yi kaffa-kaffa da hannu.
- A bar tagogi (window) a buɗe yadda iska za ta riƙa wucewa, musamman idan mai cutar ba shi kaɗai ba ne a gidan.
- Rufe hanci da nose mask a cikin taron mutane.
- Wajibi ne bin umurnin gwamnati da hukumar NCDC domin kare kai daga cutar.
Karin magana
“Rigakafi ya fi magani.”
🎯 Aiki-Tambayoyi
- A wacce ƙasa cutar ta fara ɓulla?
- Yi taƙaitaccen bayani kan cutar alaƙaƙai (Corona virus).
- Sannan kuma ka kawo hanyoyi guda uku (3) na kamuwa da kare kai daga cutar.