π¬
Hira Tsakanin Abokai Biyu
Conversation
John and Hassan meet on the way to school β a full dialogue with ten comprehension questions.
A wannan darasin zamu saurari hira ce tsakanin abokai biyu, sannan mu amsa tambayoyin da suka biyo baya.
In this lesson we listen to a conversation between two friends, then answer the questions that follow.
John da Hassan
JohnIna kwanaGood morning (how did you sleep?)
HassanLafiyaFine
JohnYa gajiyaAre you tired?
HassanBa gajiyaNot tired
JohnIna zaka?Where are you going?
HassanMakarantaTo school
HassanYa mutanen gidankuHow is your family at home?
JohnSuna lafiyaThey are well
JohnAji nawa kake?What class are you in?
HassanAji biyar (SS 2)Class five (SS 2)
JohnNa firamare ko sakandare?Primary or secondary?
HassanNa sakandareSecondary
HassanKai fa wani makaranta ka ke?And you β which school are you in?
JohnNa gama sakandareI've finished secondary
JohnYaya sunan makarantar ku?What's the name of your school?
HassanCommand SulejaCommand, Suleja
HassanKuma makarantar kwana ce ta maza da mataAnd it's a boarding school for boys and girls
HassanSunan commandant Ιin mu na yanzu Major Murtala MarafaOur current commandant is Major Murtala Marafa
JohnYaushe zaku fara jarabawa?When do your exams start?
HassanWatan gobeNext month
JohnWacce shekara za ka gama?What year will you finish?
Hassan20212021
HassanMe kake son ka karanta a jami'a?What do you want to study at university?
JohnHausaHausa
HassanNi kuma lissafiAs for me, mathematics
JohnAllah ya bamu sa'aMay God grant us good fortune
HassanAminAmen
HassanSai anjimaSee you later
JohnYauwaAlright
JohnNa godeThank you
HassanNi ma na godeThank you too
π― Aiki-Tambayoyi
Exercises & questions
- Menene sunan abokai biyun?What are the names of the two friends?
- Ina Hassan za shi?Where is Hassan going?
- A labarin wacce makaranta John yake?In the story, which school is John in?
- Menene sunan makarantar su Hassan?What is the name of Hassan's school?
- Kuma aji nawa yake?And what class is he in?
- Menene sunan shugaban makarantar?What is the name of the school's head?
- Wacce shekara Hassan za gama sakandare?What year will Hassan finish secondary school?
- Yaya yanayin makarantar su Hassan take?What kind of school is Hassan's?
- Me Hassan ke son ya karanta?What does Hassan want to study?
- Me John ke son karanta a Jami'a?What does John want to study at university?