Rukunonin Kalmomin Hausa
Parts of Speech
Noun, pronoun, verb, adjective and adverb, each with example sentences.
Rukunonin kalmomi sune tubalin ginin jimlar Hausa, misali suna, aikatau, da sauransu. Ga bayanansu dalla-dalla.
Suna (Noun): Suna kalma ce da ke nuni da sunayen mutane, dabbobi, wurare, da abubuwa. Misali: Adama, makaranta, ds.
Nau'in suna
Kinds of noun
- MutanePeople
- DabbobiAnimals
- WurarePlaces
- AbubuwaThings
Misalansu cikin jimloli
Nouns in sentences
- Suna na Asabe.
- Mun sayi rago.
- Baba ya je Abuja.
- Na sa agogo.
Wakilin Suna (Pronoun): Wakilin suna, sunaye ne da ake amfani da su a maimakon suna. Misali: ni, mu, ku, shi, da sauransu.
Wakilan suna
Pronouns
- Ni
- na
- ta
- kai
- shi
- ke
- ita
- mu
- ku
- su
- Me
- wa
- wanne
- wacce
- wannan
Misalansu cikin jimloli
Pronouns in sentences
- Ni na yi rubutu.
- Ta zo tun jiya.
- Wanene babba a cikin ku?
- Shi ya zo na farko.
Aikatau (Verb): Kamar yadda sunan yake, kalmar aikatau an samo ta ne daga kalmar aiki. Aikatau kalmomi ne masu nuni da aiki a jimla, misali rubutu, ds.
Kalmomin aikatau saukaƙa
Simple verbs
- Ci
- sha
- tashi
- zama
- gudu
- kallo
- wasa
- Karatu
- rubutu
- magana
- tafiya
- kwanciya
- Sauraro
- yanka
- girki
- bacci
- dariya
- tsalle
- shara
Misalansu cikin jimloli
Verbs in sentences
- Lanzina ta na girki.
- Anisa ta iya tafiya.
- Manu ya yanka kaza.
- Malami yana rubutu.
- Sani ya yi wanka.
Siffatau (Adjective): Siffatau kalmomi ne masu ƙarin bayani a kan suna, misali dogo, fari, da sauransu.
Kalmomin siffatau
Adjectives
- Dogo
- gajere
- ramamme
- siriri
- kyakkyawa
- fari
- kore
- ja
- sabo
- tsoho
- babba
- ƙarami
Misalansu a jimla
Adjectives in sentences
- Zinatu doguwa ta zo.
- Ta sha ruwa da sabon kofi.
- Ramlatu kyakkyawa ce.
- Yaya ya sayo sabon mota.
Bayyanau (Adverb): Bayyanau kalmomi ne da ke ƙarin bayani a kan aikatau, misali safe, ds.
Nau'in bayyanau
Kinds of adverb
- Bayyanau na WuriPlace
- Bayyanau na LokaciTime
- Bayyanau na YanayiManner
Misalansu cikin jimloli
Adverbs in sentences
- Malam na rubutu da sauri.
- Hassan ya yanka rago da safe.
- Baba na tafiya a hankali.
- Sun iso jiya da yamma.
🎯 Aiki-Tambayoyi
- Kawo misalan jimloli da sunan mutum, dabba, wuri da abubuwa, kowanne guda huɗu (4).
- Kawo misalan jimloli da kalmomi siffatau guda biyar (5).
- Da kuma misalan jimloli da kalmomin aikatau biyar (5).