Hira Tsakanin Abokai Biyu
ConversationJohn and Hassan meet on the way to school — a full dialogue with ten comprehension questions.
A wannan darasin zamu saurari hira ce tsakanin abokai biyu, sannan mu amsa tambayoyin da suka biyo baya.
In this lesson we listen to a conversation between two friends, then answer the questions that follow.
John da Hassan
- John
- Ina kwanaGood morning (how did you sleep?)
- Hassan
- LafiyaFine
- John
- Ya gajiyaAre you tired?
- Hassan
- Ba gajiyaNot tired
- John
- Ina zaka?Where are you going?
- Hassan
- MakarantaTo school
- Hassan
- Ya mutanen gidankuHow is your family at home?
- John
- Suna lafiyaThey are well
- John
- Aji nawa kake?What class are you in?
- Hassan
- Aji biyar (SS 2)Class five (SS 2)
- John
- Na firamare ko sakandare?Primary or secondary?
- Hassan
- Na sakandareSecondary
- Hassan
- Kai fa wani makaranta ka ke?And you — which school are you in?
- John
- Na gama sakandareI've finished secondary
- John
- Yaya sunan makarantar ku?What's the name of your school?
- Hassan
- Command SulejaCommand, Suleja
- Hassan
- Kuma makarantar kwana ce ta maza da mataAnd it's a boarding school for boys and girls
- Hassan
- Sunan commandant ɗin mu na yanzu Major Murtala MarafaOur current commandant is Major Murtala Marafa
- John
- Yaushe zaku fara jarabawa?When do your exams start?
- Hassan
- Watan gobeNext month
- John
- Wacce shekara za ka gama?What year will you finish?
- Hassan
- 20212021
- Hassan
- Me kake son ka karanta a jami'a?What do you want to study at university?
- John
- HausaHausa
- Hassan
- Ni kuma lissafiAs for me, mathematics
- John
- Allah ya bamu sa'aMay God grant us good fortune
- Hassan
- AminAmen
- Hassan
- Sai anjimaSee you later
- John
- YauwaAlright
- John
- Na godeThank you
- Hassan
- Ni ma na godeThank you too
Aiki-Tambayoyi
Exercises & questions
- Menene sunan abokai biyun?What are the names of the two friends?
- Ina Hassan za shi?Where is Hassan going?
- A labarin wacce makaranta John yake?In the story, which school is John in?
- Menene sunan makarantar su Hassan?What is the name of Hassan's school?
- Kuma aji nawa yake?And what class is he in?
- Menene sunan shugaban makarantar?What is the name of the school's head?
- Wacce shekara Hassan za gama sakandare?What year will Hassan finish secondary school?
- Yaya yanayin makarantar su Hassan take?What kind of school is Hassan's?
- Me Hassan ke son ya karanta?What does Hassan want to study?
- Me John ke son karanta a Jami'a?What does John want to study at university?