Darussan Hausa L2 Kumshiya Harrufa Tatsuniya

← Kumshiya

Darasi 14 · Shafi 18–19

Abincin Hausawa Da 'Ya'yan Itatuwa

Dishes and Fruits

Everyday dishes, fruits, and the table manners that go with them.

Kamar sauran al'umma, Hausawa ma ba a bar su a baya ba, domin suna da abinci da 'ya'yan itatuwa iri daban-daban. Ga misalansu.

Abincin ci da sha

Food and drink

  • Tuwo da miya stiff grain porridge with soup
  • Masa da miya rice cakes with soup
  • Gurasa da taushe flat wheat bread with pumpkin stew
  • Shinkafa da mai da yaji rice with oil and spice
  • Burabisko fried dough snack
  • Kosai bean-flour fritters
  • Fura da nono millet balls with fermented milk

'Ya'yan Itatuwa

Fruits

  • Abarba pineapple
  • Agwaluma wild custard-apple
  • Gwaiba guava
  • Ayaba banana
  • Kankana watermelon
  • Lemo orange
  • Mangwaro mango
Hotuna
Food and fruit photographs

A plate of rice with spiced sauce, a plate of tuwo, and a still life of watermelon, mango, bananas, orange and pineapple.

Image not included — text placeholder

Ɗabi'un cin abincin Hausawa

Table manners

  • Yi ma na kusa tayi — invite the person beside you.
  • Ci da hannun dama — eat with the right hand.
  • Zama da kalmashe ƙafa — sit properly with the legs folded.
  • Riƙe kwano lokacin da ana cin abinci — hold the bowl steady while eating.
  • Wanke hannu kafin da bayan gama cin abinci — wash hands before and after.

Aiki-Tambayoyi

  1. Lissafo abincin Hausawa guda uku (3) da 'ya'yan itatuwa guda huɗu (4) bayan wanda muka nazarta a aji.
  2. Sannan da wasu ɗabi'un cin abincin Hausawa guda biyu (2).
  3. Yi bayani a taƙaice yadda ake yin masa (waina).