Sadarwa
CommunicationModern and traditional ways of carrying a message.
Sadarwa hanya ce ta isar da saƙo tsakanin mutane biyu ko fiye da haka. Akan yi amfani da hanyoyin sadarwa domin isar da saƙo tsakanin mutanen da ke nisa da juna, misali gari zuwa gari ko jihohi da sauransu.
Muna da ire-iren sadarwa guda biyu: na zamani da na gargajiya.
Sadarwa ta zamani
Modern communication
- Rediyo radioAna amfani da rediyo don sauraron labarai da sanarwa.
- Talabijin televisionNa kama tashoshin gida da waje don ji da kuma kallon yadda abubuwa ke gudana a duniya.
- Wayar-hannu mobile phoneDon magana da tura saƙon wasiƙa.
- Allon sadarwa notice boardNa amfani wajen aika saƙo ko talla ga jama'a.
- Jaridu da mujallu newspapers and magazines
- Shafukan yaɗa zumunta social mediaKamar su facebook, ds.
- Wasiƙa letter
Sadarwa ta gargajiya
Traditional communication
- Ƙaho horn
- Bindiga gun
- Hayaƙi smoke signal
- Shela public crier
Akan yi amfani da ƙaram bindiga ko shela ko kuma hayaƙi don sanar da mutane wani saƙo, ko kuma don shirin yaƙi ko faraut a zamanin da.
A stack of newspapers, a portable radio, a mobile phone, a long-barrelled hunting gun and a traditional side-blown horn.
Image not included — text placeholderAiki-Tambayoyi
- Kawo misalan shafukan yaɗa zumunta guda uku (3).
- Lissafo muhimmancin sadarwa guda uku (3).