Darussan Hausa L2 Kumshiya Harrufa Tatsuniya

← Kumshiya

Darasi 8 · Shafi 12

Lokutan Agogo

Clock Timing

Telling the time in Hausa: karfe, kwata, rabi, saura and minti.

Lokutan agogo darasi ne da ke koyar da yadda ɗalibai za su fahimci kuma su faɗi lokaci a Hausance.

Ga wasu kalmomi da Hausawa ke amfani da su: dakika, minti, kwata, rabi, saura, sa'a, dai-dai, da sauransu.

Ga misalan agoguna suna nuna lokuta daban-daban.

Kalmomin lokaci

Time words

  • Dakika second
  • Minti minute
  • Sa'a hour
  • Kwata quarter
  • Rabi half
  • Saura remaining, “to” the hour
  • Dai-dai exactly, on the dot

Misalan agogo

Clock faces shown in the book

  • Ƙarfe shida dai-dai 6:00 exactly
  • Ƙarfe uku da rabi 3:30
  • Ƙarfe huɗu saura minti biyar 4:55 — five minutes to four's hour count
  • Ƙarfe goma da kwata 10:15
  • Ƙarfe tara da minti ashirin 9:20
Hoto
Ƙarfe shida dai-dai
Ƙarfe uku da rabi
Ƙarfe huɗu saura minti biyar
Ƙarfe goma da kwata
Ƙarfe tara da minti ashirin
Five clock faces

Line drawings of analogue clocks set to 6:00, 3:30, 4:55, 10:15 and 9:20, each captioned in Hausa.

Aiki-Tambayoyi

  1. Yi amfani da misalan da muka kawo, ka sa waɗannan lokutan cikin agogo: 12:00, 12:45, 7:20, 8:50, 2:20.