Lokutan Agogo
Clock TimingTelling the time in Hausa: karfe, kwata, rabi, saura and minti.
Lokutan agogo darasi ne da ke koyar da yadda ɗalibai za su fahimci kuma su faɗi lokaci a Hausance.
Ga wasu kalmomi da Hausawa ke amfani da su: dakika, minti, kwata, rabi, saura, sa'a, dai-dai, da sauransu.
Ga misalan agoguna suna nuna lokuta daban-daban.
Kalmomin lokaci
Time words
- Dakika second
- Minti minute
- Sa'a hour
- Kwata quarter
- Rabi half
- Saura remaining, “to” the hour
- Dai-dai exactly, on the dot
Misalan agogo
Clock faces shown in the book
- Ƙarfe shida dai-dai 6:00 exactly
- Ƙarfe uku da rabi 3:30
- Ƙarfe huɗu saura minti biyar 4:55 — five minutes to four's hour count
- Ƙarfe goma da kwata 10:15
- Ƙarfe tara da minti ashirin 9:20
Ƙarfe shida dai-dai
Ƙarfe uku da rabi
Ƙarfe huɗu saura minti biyar
Ƙarfe goma da kwata
Ƙarfe tara da minti ashirin
Line drawings of analogue clocks set to 6:00, 3:30, 4:55, 10:15 and 9:20, each captioned in Hausa.
Aiki-Tambayoyi
- Yi amfani da misalan da muka kawo, ka sa waɗannan lokutan cikin agogo: 12:00, 12:45, 7:20, 8:50, 2:20.