Darussan Hausa L2 Kumshiya Harrufa Tatsuniya

← Kumshiya

Darasi 5 · Shafi 8

Hira Tsakanin Abokai Biyu

Conversation

John and Hassan meet on the way to school — a full dialogue with ten comprehension questions.

A wannan darasin zamu saurari hira ce tsakanin abokai biyu, sannan mu amsa tambayoyin da suka biyo baya.

In this lesson we listen to a conversation between two friends, then answer the questions that follow.

John da Hassan

John
Ina kwanaGood morning (how did you sleep?)
Hassan
LafiyaFine
John
Ya gajiyaAre you tired?
Hassan
Ba gajiyaNot tired
John
Ina zaka?Where are you going?
Hassan
MakarantaTo school
Hassan
Ya mutanen gidankuHow is your family at home?
John
Suna lafiyaThey are well
John
Aji nawa kake?What class are you in?
Hassan
Aji biyar (SS 2)Class five (SS 2)
John
Na firamare ko sakandare?Primary or secondary?
Hassan
Na sakandareSecondary
Hassan
Kai fa wani makaranta ka ke?And you — which school are you in?
John
Na gama sakandareI've finished secondary
John
Yaya sunan makarantar ku?What's the name of your school?
Hassan
Command SulejaCommand, Suleja
Hassan
Kuma makarantar kwana ce ta maza da mataAnd it's a boarding school for boys and girls
Hassan
Sunan commandant ɗin mu na yanzu Major Murtala MarafaOur current commandant is Major Murtala Marafa
John
Yaushe zaku fara jarabawa?When do your exams start?
Hassan
Watan gobeNext month
John
Wacce shekara za ka gama?What year will you finish?
Hassan
20212021
Hassan
Me kake son ka karanta a jami'a?What do you want to study at university?
John
HausaHausa
Hassan
Ni kuma lissafiAs for me, mathematics
John
Allah ya bamu sa'aMay God grant us good fortune
Hassan
AminAmen
Hassan
Sai anjimaSee you later
John
YauwaAlright
John
Na godeThank you
Hassan
Ni ma na godeThank you too

Aiki-Tambayoyi

Exercises & questions

  1. Menene sunan abokai biyun?What are the names of the two friends?
  2. Ina Hassan za shi?Where is Hassan going?
  3. A labarin wacce makaranta John yake?In the story, which school is John in?
  4. Menene sunan makarantar su Hassan?What is the name of Hassan's school?
  5. Kuma aji nawa yake?And what class is he in?
  6. Menene sunan shugaban makarantar?What is the name of the school's head?
  7. Wacce shekara Hassan za gama sakandare?What year will Hassan finish secondary school?
  8. Yaya yanayin makarantar su Hassan take?What kind of school is Hassan's?
  9. Me Hassan ke son ya karanta?What does Hassan want to study?
  10. Me John ke son karanta a Jami'a?What does John want to study at university?