Darussan Hausa L2 Kumshiya Harrufa Tatsuniya

← Kumshiya

Gabatarwa

Preface

Da sunan Allah (Ubangiji) mai rahama mai jin ƙai, tsira da aminci su ƙara tabbata ga Annabi Muhammad. Na rubuta wannan littattafi mai suna DARUSSAN HAUSA L2 ne don malamai da ɗalibai masu nazarin harshen Hausa a matakin ƙananan makarantun sakandare, da fatan zai taimake su wajen koyo da koyarwa.

Dangane da tsarin littafin, ya ƙunshi darussa ne kan harshen Hausa L2, wato harshen magana na biyu, a matakin ƙananan makarantun sakandare. Littafin ya dace da sharaɗɗodi da sabon manhajar Hausa L2 na Hukumar Bincike Da Bunƙasa Ilimi Ta Najeriya (NERDC), wanda yake canzawa lokaci zuwa lokaci. An ƙawata littafin da kyawawan hotuna don jawo hankali da saukaƙa fahimtar ɗalibai.